Afirka ta Kudu Ta Janye Sojojinta Daga tawagar MONUSCO

Afirka ta Kudu ta sanar cewa za ta janye sojojinta kusan 700 da aka tura tare da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD wato

Afirka ta Kudu ta sanar cewa za ta janye sojojinta kusan 700 da aka tura tare da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD wato MONUSCO, a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Wannan shawarar, ta zo ne yayin da gabashin kasar ke ci gaba da fuskantar tashin hankali daga kungiyar M23 da kuma rikice-rikicen da suka ci gaba da faruwa tsawon shekaru talatin.

Afirka ta Kudu ta sanar cewa Za a mayar da sojojin kasar kimanin 700, daga cikin jimillar sojojin 12,500, a hankali kafin karshen shekara.

A cewar Pretoria, wannan shawarar tana da nufin “hada karfi da kuma tsara rundunar tsaron Afirka ta Kudu” bayan shekaru ashirin da bakwai na aikin wanzar da zaman lafiya a DRC.

Shugaba Cyril Ramaphosa ya sanar da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres a hukumance game da niyyar kasarsa ta janye sojojinta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted