Kagame: Rikicin Rwanda da Congo Batun Tsaro Ne Ba Mamaye Albarkatu Ba

Shugaban Rwanda Paul Kagame ya bayyana cewa tashe-tashen hankula tsakanin ƙasarsa da Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo ba su da alaƙa da albarkatun ƙasa ko mamaye yankuna

Shugaban Rwanda Paul Kagame ya bayyana cewa tashe-tashen hankula tsakanin ƙasarsa da Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo ba su da alaƙa da albarkatun ƙasa ko mamaye yankuna a gabashin Kongo. Ya jaddada cewa tushen  matsalar da cewa  tana tattare da rundunar sojin kasar ta Congo.

A lokacin buɗe taron tattaunawa na ƙasa na shekara-shekara a birnin  Kigali, Kagame ya fayyace cewa batun “ba batun ma’adanai ba ne,” yana mai bayayya cewa idan Rwanda tana cikin Kongo don albarkatunta, “da yanzu ta mallaki arziki da ya ninka wanda take da shi sau ɗari.” Ya jaddada cewa abin da ƙasarsa ta bayyana a matsayin “matakan kariya” martani ne ga barazanar da ke ci gaba da fitowa daga gabashin Kongo.

Jawabin Kagame ya biyo bayan zargin da shugaban Kongo Félix Tshisekedi ya yi cewa Rwanda tana neman raba ƙasarsa da kuma mamaye  yankin gabashinta mai arzikin albarkatu.

Ƙungiyar M23 tana taka Babbar rawa a rikicin gabashin Kongo, inda Majalisar Dinkin Duniya da ƙasashen Yamma ke zargin Rwanda da goyon bayanta, zargin da Kigali ta musanta.

Hakazalika, Tshisekedi ya yi kira da a rage tashin hankali da kuma haɗin gwiwa don cimma zaman lafiya, yayin da Ma’aikatar Harkokin Wajen Rwanda ta yi watsi da waɗannan kiraye-kirayen tare da bayyana su a matsayin na matsayin na  siyasa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted