Hamas Ta yi Tir Da Hare-haren Bayan bayan Nan Da HKi Ta Kai A Yankin Gaza

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi tir da mummunan harin da HKI takai a yankin Gaza wanda akalla ya kashe falasdinawa 23,

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi tir da mummunan harin da HKI takai a yankin Gaza wanda akalla ya kashe falasdinawa 23, a daya daga cikin hari mafi muni da ta kai tun bayan kulla yarjejeniyar dakatar da bude wuta a watan oktoba, kuma ta ce harin ya kara tabbatar da kisan kare dangi da HKI ke yi kan alummar Gaza.

wadannan hare haren ya kara nuna bakar aniyar Natanyaho na kokarin kawo cikas da gangan wajen hana aiki da bangare na biyu na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma, musamman bayan sake bude mashigar rafah.

Akalla mutane 14 ne suka mutu a harin da Isra’ila ta kai a yankin Tuffa da zaitun dake makwabtaka da yankin Gaza, haka zalika wasu guda 4 na daban ma an bada rahoton sun rasu a wani harin da isra’ila ta kai a wani tanti da  yan’ gudun hijira ke zaune a yankin qizan abu rashwan dake kudancin khan yunus a kudancin gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted