Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Arakci ya bayyana cewa; Kamar yadda aka tsara za a yi zaman tattaunawa akan Nukiliya tare da Amurka a ranar Juma’a da misalin karfe 10;00 am a birnin Muscat.
Arakci ya kuma ce’ Muna yin godiya ga ‘yan’uwanmu mutanen Oman saboda tsara dukkanin shirye-shiryen da su ka kamata.
A shekaran jiya ne Talata ne dai Iran ta bukaci ganin an sauya wurin yin taron daga Istanbul na kasar Turkiya, zuwa birnin Muscat na kasar Oman. Haka nan kuma Iran din ta ce, tattaunawar za ta mayar da hankali ne akan batun Nukiliya kadai ba wani abu ba.
Sanarwar ta Ministan harkokin wajen Iran ta zo ne bayan da a jiya wasu kafafen watsa labaru su ka rika yada cewa an dage tattaunawar.