Wani bafalasdine Khalid Saifi wanda ya dade yana tsare a gidan yarin yahudawan Isra’ila ya rasu kwanaki kadan bayan sakinsa saboda azabtarwa da suka yi masa a lokacinda yake tsare.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Khalid Al-Saifi wanda yake zaune a sansanin yan gudun hijira na Dheisheh a kusa da garin Bethlahem a yankin yamma da kogin Jordan, ya rasu mako guda kacal bayan da gwamnatin HKI ta sallameshi daga gidan yari.
Hukumar fursinoni ta Palasdinawa ta bada sanarwan cewa tun bayan sakinsa, Khalil A-shaifi bai da lafiya kuma rashin lafiyarsa ya ci gaba da tabarbarewa har zuwa rasuwarsa a wani asbiti a yankin yamma da kogin Jordan .
Sun kuma bada sabarwab cewa sojojin yahudawan sun yi masa allura wanda suka ce na mura ne sannan suka sake yi masa wata wanda ya jawo kumburari a jikinsa sannan suka tura shi asbiti a cikin gidan yarin. Daga
Al-sifidai yana watani hudu yana tsare a hannun yahudawa, bayan sun dade suna neman sa. Hukumar tana ganin yahudawan ne suka kashe shi irin kisa ba na lokaci guda ba.