Ministan Harkokin Waje Abbas Araghchi ya ce Iran a shirye take koyaushe don tattaunawa bisa girmama juna, amma Jamhuriyar Musulunci ba za ta yi shawarwari ba a karkashin matsin lamba da barazana ba.
Araghchi ya yi wannan jawabin ne yau Litinin yayin da shi da abokan aikinsa a Ma’aikatar Harkokin Waje suka sabunta biyayyarsu ga manufofin Imam Khomeini, wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci, a kabarin sa da ke kudancin Tehran.
Ya ce yanzu makiya suna magana game da diflomasiyya bayan gazawar makircin da suka yi wa Iran a bara, gami da cin zarafi daga Amurka da Isra’ila, da kuma tashe-tashen hankulan ta’addanci.
“Diflomasiyya ba ta dace da matsin lamba, da barazana ba, kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata ci gaba a wannan hanya cikin jajircewa da karfi,” in ji ministan harkokin wajen Iran.
Da yake magana game da tarzomar da ke da alaka da kasashen waje ta kwanan nan, babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce tarzomar ba ta da alaƙa da zanga-zangar lumana da aka amince da ita a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulki.
A tsawon tarzomar da kuma bayan abubuwan da suka faru, Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Iran.