Shugaban kasar Kongo Yana Son A Cimma Zaman Lafiya Bayan Ya Sanya sharudda

Shugaban kasar DR Congo Félix chisekidi jim kadan bayan ganawa da tawagar sassanta rikici da kasar ke fama da shi da Rwanda,ya jaddada farin cikinsa

Shugaban kasar DR Congo Félix chisekidi jim kadan bayan ganawa da tawagar sassanta rikici da kasar ke fama da shi da Rwanda,ya jaddada farin cikinsa da kuma fatan ganin an cimma zaman lafiya mai dorewa, duk da cewa ya shimfida  wasu sharudda a gaban  tawagar da kungiyar Afrika ta aike zuwa kasar.

Félix Tshisekedi ya bayyana fatan ganin bangarorin sun amince da sakamakon zabe ba tare da kalubalantar hukumar ba, bugu da kari, shugaban ya ki amincewa da tsarin zuwa wata kasa domin warware wasu daga cikin matsaloli da ya dace a tsaya a gida domin tattaunawa a kai.

haka zalika  ya ce “Idan za a gudanar da wannan tattaunawar, za a gudanar da ita a kasar ne kuma hukumomi tare da hadin gwiwar kungiyoyi da shugabanin addinai , za a zauna da nufin shirya yada abubuwa za su gudana.

Tsawon shekaru Rwanda da DRCongo na zargin junansu da taimakawa kungiyoyi masu dauke da makamai, Shugaban Amurka Donald Trump ya taka muhimiyar rawa don ganin an magance wannan rikici na tsawon shekaru.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted