An Yi Tattaunawa Ta Wayar Tarho Tsakanin Shugabannin Kasashen Iran Da Masar

A jiya Asabar da dare ne dai aka yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakanin shugabannin Iran Mas’ud Fizishkiyan da takwaran na kasar Masar Abdulfattah

A jiya Asabar da dare ne dai aka yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakanin shugabannin Iran Mas’ud Fizishkiyan da takwaran na kasar Masar Abdulfattah al-sisy akan halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya.

Shugaban kasar ta Iran ya yi jinjina ga shugaban kasar Masar saboda kokarin da kasarsa take yin a son ganin an rage zaman dar-dar a wannan yankin, da kuma nuna goyon da take yi wa jamhuriyar musulunci ta iran.

Har ila yau shugaban kasar ta Iran ta bukaci ganin kasashen biyu sun bunkasa alaka a tsakaninsu a karkashin dankon zumuncin dake a tsakanin kasashen musulmi.

Bugu da kari shugaba Mas’ud Fizishkiyanya yi Ishara da yadda Amurka da Haramtacciyar kasar Isra’ila suke ci gaba da rikita wannan yankin da kokarin haddasa wani sabon yakin. Haka nan kuma ya bayyana yadda matsin lamba mai tsanani na tattalin arziki akan Iran ya jawo rikice-rikicen bayan nan da su ka faru a cikin kasar.

Shugaba Mas’ud Fizishkiyan ya kuma ce, ko kadan Iran ba ta maraba da yaki,domin ta yi Imani da cewa yaki ba zai amfani kowa ba, ba Iran ba, ba Amurka ba, ba kuma wannan yankin ba.

A nashi gefen shugaban kasar Masar ya nuna gamsuwarsa da tattaunawa da shugaban kasar ta Iran, sannan kuma ya yi wa al’ummar Iran, mai tsawon tarihi fatan zaman lafiya da tsaro.

Haka nan kuma ya ce, barkewar wani sabon rikici ba Iran kadai zai cutar ba, zai shafi wannan yankin ne baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted