Jiragen saman Isra’ila sun kashe akalla mutane 30 a Zirin Gaza, daya daga cikin adadi mafi muni tun bayan tsagaita wuta a watan Oktoban 2025 da nufin kawo karshen yakin.
Jami’an kiwon lafiya a Falasdinu sun ce akalla mutane 26, ciki har da yara, sun mutu a ranar Asabar din nan, a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza.
Akalla shida daga cikin wadanda sojojin gwamnatin Isra’ila suka kashe a Gaza yara ne, kamar yadda ma’aikatar agajin gaggawa ta ruwaito.
Wani harin sama da Isra’ila ta kai kan wani tanti da ke dauke da mutanen da suka rasa matsuguni a yankin al-Mawasi da ke arewa maso yammacin birnin Khan Younis ya kashe akalla Falasdinawa bakwai, ciki har da yara uku, kamar yadda majiyoyin lafiya suka ruwaito.
A cewar Ofishin Yada Labarai na Gwamnatin Gaza, akalla Falasdinawa 524 ne suka mutu sakamakon harin da sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta jagoranta a Gaza ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran sake bude hanyar Rafah, wadda ta hada Gaza da Masar, a gobe Lahadi a karon farko tun bayan rufe ta a watan Mayun 2024.
Mashigar Rafah ita ce babbar hanyar shiga Gaza ga Falasdinawa don samun agajin kasa da kasa da kayayyakin agaji.
Sake bude hanyar Rafah wani bangare ne na yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta jagoranta.