Afirka ta Kudu ta kori karamin jakadan Isra’ila

Afirka ta Kudu ta umarci mataimakin jakadan Isra’ila da ya bar kasar cikin awanni 72. Ana zargin Ariel Seidman, da lalata dangantaka tsakanin kasashen biyu

Afirka ta Kudu ta umarci mataimakin jakadan Isra’ila da ya bar kasar cikin awanni 72.

Ana zargin Ariel Seidman, da lalata dangantaka tsakanin kasashen biyu ta hanyar wallafa kalaman batanci game da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a shafukan sada zumunta da kuma karya ka’idojin diflomasiyya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Afirka ta Kudu ta ayyana shi a matsayin wanda ba a maraba da shi.

Mista Seidman shi ne babban jami’in diflomasiyyar Isra’ila a Afirka ta Kudu tun bayan da aka kira jakadan Isra’ila a shekarar 2023.

A martanin da ta mayar, Ma’aikatar Harkokin Wajen Isra’ila ta sanar a ranar X cewa za ta kori wani babban jami’in diflomasiyyar Afirka ta Kudu, Shaun Edward Byneveldt, tare da umurtarsa ​​da ya bar Isra’ila cikin awanni 72.

Dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu ta yi tsami tun lokacin da Afirka ta Kudu ta kai ƙarar kisan kare dangi ga Kotun Duniya kan ayyukan Isra’ila a Gaza.

Isra’ila ta musanta zarge-zargen sosai kuma ta zargi Afirka ta Kudu da yin aiki a matsayin bangaren shari’a na kungiyar Hamas ta Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted