Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 190

190-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikinshirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo

190-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikinshirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///… madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin siarar Imam Al-Hassan (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da magana dangane da siyasar Iyalan gidan manzon Allah (s) a gaban irin siyasar Mu’awiya  dan Abusufyan da shi da ma’aikatansa a lokacin da al-amuran shugabancin al-ummar Musulmi suka koma hannusa.

A cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da magana dangane da siyasarsu, kan ma’aikatansu, wadanda suke taimaka masu wajen gudanar da harkokin al-umma daga wuraren da suke nesa daga inda suke. Mun kawo misalai kan yadda Imam Ali (a) yake da wadanda suke kawo masa labara kan abubuwan da ma’aikatansa suke yi, sannan yakan dauki mataki a kan duk wanda ya tabbatar da cewa yana zaluntar mutane, ko kuma yana cin kudaden jama’a.

Yakan kuma aika masu wasiku ya gargadesu kan cin hanci da rashawa, ya kuma koya masu yadda zasu yi mu’amala da mutane daban-daban a inda suke shugabanci.

Banda haka mun yi magana dangane da siyasarsu ta ‘rashin tilastawa wani zuwa yaki, sai dai sai su kodaitar da su yin haka. Sabanin abinda Mu’awiya da Banu uamayya suka aikata a duk tsawon shugabancinsu.

Sannan daga karshe mun fara magana kan siyasarsu dangane da kashe dukiyar mutane, ko kuma kudaden Jama’a. Inda muka bayyana irin tsentsenin da suke yi wajen kashe kudaden jama’a. Mun ji yadda Imam Ali (a) ya kashe fitillan jama’a bayan ya fahinci cewa Talha da zubair sun zo masa da dare don wata magana da ta shafesu ne. Sannan kuraishawa sun yi fushi da shi a lokacinda yaki amincewa ya fafitasu a kan sauran musulmi wadanda ba kurashawa ba, ko kuma wadanda ba larabawa ba, a rabon kudade.

A wajen Iyalan gidan manzon Allah (s), dukiyar al-umma dole ne a kashe su don masalahar al-umma gaba daya, kuma bawa shuwagabanni kabilu ko manya-manyan mutane dukiyar al-umma, zalunci ne. wadanda suka cancanci samun kudaden al-imma su ne talakawansu, ko kuma don masalahar kowa.

Bai kamata shugaban gwamnatin musulunci ya kebe kansa da wani bangare mai yawa na dukiyar al-umma ba.  Ko kuma ya zabi wasu daga cikin danginsa ya arzutasu da su ba. Ko kuma ya arzuta wadanda suke kusa da shi da wadan nan kudade ba.

Wannan a wajen iyalan gidan manzon Allah (s) kha’inci ne ga Allah ga kuma musulmi kamar yadda muka bayyana a baya.  Wannan siyasar Amirul muminina (a) ya tafiyar da ita a cikin shekaru 4 da watanni 9 da yayi yana khalifan musulmi. Kamar yadda muka fada da wannan siyasar ya shafe talauci a cikin bangaren daular musulunci wanda yake karkashin ikonsa a lokacin.

Amirul mumina misali ne a shugabancin iyalan gidan manzon Allah (s) a bayansa, don shi ne kadai ya sami damar shugabantar al-ummar musulmi na lokaci mai tsawo. Kuma da Imam Al-Hassan (a) da kuma Imam Al-Hussain (a) ko kuma daya daga cikin wadan nan limamai 9 sun sami daman shugabancin al-ummar musulmi. Babu wani bambanci da za’a gani sai na zamanin da suka sami wannan damar. Amma shugabancin iri daya ne.

Amirul muminina (a) yayi zuhudu, ko gudun duniya a lokacinda dukiyar daula mafi girma a duniya a lokacin yana hannunsa. Haruna ya ruwaito daga babanta Antarah ya ce: na shiga wajen Aliyu (a) a wani wuri da ake kira Khurnuq, yana sanye da wata tsohuwar rigar fata, yana karkawa (saboda sanyi) a lokacin ana sanyi, sai na ce masa: Ya shugaban muminai! Allah ya sanya maka da iyalanka rabo a cikin wannan dukiyar, me ya sa kake haka da kanka?.

{Wallah ban baku kome ba, don haka wannan rigar fata tace da na fito da ita daga madina}

Amirul muminina (a) bai da ragan sanyin da zai sa ya kare shi daga sanyi, sai wata rigar fata wacce ya fito da ita daga Madina, sannan yana iya sa rigar al-hariri ko dibaji ko kuma riga mai kyau a cikin rabonsa a cikin dukiyar da ke hannunsa. Amma saboda gudun duniya ba zai sa ba. Haka ma baya barin iyalan gidansa su sanya riga mai tsada.

Abu rafiu, ya ruwaito hadisi, (a lokacin shi ne mai kula da baitul Mali a kufa) yana cewa wata rana Amirulmuminina (a) ya shiga waje na, a lokacin na bawa daya daga cikin yayansa mata lulu’u daga baitul Mali, ( ta sanya a wuyarta) sai ya ganta ya kuma ganeta, sai fuskansa ta canza, hankalinsa ya tashi, sai yace, ina ta sami wannan? Wallah zan yanke hannunta!. A lokacinda Abu Rafiu ya ga cewa da gaske yake, sai yace, nine na bada ya Amirulmuminina don nag anta, bata da kome a wuyanta, … sai yace naga ya nutsu.

Sannan ya ce: Hakika na auri Fatimah (s) bani da shimfida sai fatar rago cce muke barci a kanta da dare….bamu da mai khidima sai ita}

Wannan shi ya sa bayyana amincewa ya zabi diyarsa ta sa wannan lulu’un kan sauran matan musulmi. Wannan shi ne karshen adalci wanda wani bai taba yin irinsa ba.

Yana daga cikin tsentseninsa da kuma daidaito tsanani tsakanin musulmi,Asim dan Kalib ya ruwaito daga babansa yana cewa: An kawowa Ali(a) dukiya daga Esfahan, sai ya rata na kashi 7, sai ga ya bredi a cikinta, sai ya Rabara 7 itama, sai ya kira wata  jama’a sannan ya yi kuri’a a tsakaninsu don ya gano wanda zai fara bawa.

Wannan shi ne Amirul mumina (a) wanda ya zama babban misali a shugabancin iyalan gidan manzon Allah (s) a shugabanci da kuma siyasar addinin musulunci na gaskiya.

Da Imam Hassan (a) zai bi hanyoyi wadanda ba wanda mahaifinsa da kuma manzon Allah (s) suka bi ba, da yana iya samun sarauta, da ya kashe kudade ta hanyar da bai dace ba kamar yadda mu’awiya yayi, da ba zai sami galaba a kansa ba. Amma ya zabi kare addinin musulunci daga gurbata. Ya zabi bin hanya wacce Allah Ta’ala ya zabawwa wakilansa a bayan kasa wajen tafiyar da al-amuran al-ummar musulmi, shi ya sa kuma Mu’awiya  ya sami galaba a kansa.

Sai kuma dangane da sulhun da Imam Al-Hassan (a) yayi da Mu’awiya dan Abusfyan. Ma;aman tarihi sun yi sabani mai yawa kan wanda ya fara neman sulhuntawa tsakanin bangarorin biyu.

Ibnu Khaldun da wadanda suka tafi kan ra’ayinsa ya bayyana cewa Imam Al-Hassan ne y afara neman sulhuntawa da Mu’awiya bayan da al-amuran sosjojinsa sun lalace ha rya kaiga ya nebe kauna daga yakar mu’awiya da su.

Wasu kuma sun tafi a kan cewa Mu’awiya ne ya fara nemen sulhuntawa da shi (a) a cikin wasikun da ya aiko masa inda a cikinsu ya yi barazanar kashe shi idan yaga dama saboda yana da wadanda zasu kashe shi a cikin sojojinsa.

Ibn Khaldun yace: A lokacinda aka dabawa Imam Al-Hassan wuka a cinyarsa a Mada’inc, ya kira Amru dan Salmata Al-Arhabi ya aike shi zuwa wajen Mu’awiya tare da wasu sharudda.

Sai kuma mai Kamil Fittarikh y ace: Ana iya hada al-amuran guda biyu duka, wato da farko Mu’awiya ya aika masa da wasika da farko sannan shi kuma ya mayar masa da dan sakon da ya aika dauke da sharuddansa(a).

Amma sibdu ibn Al-Jauzi y ace : Mu’awiya ya Aikawa Imam Al-Hassan (a) wasika a asirce, amma bai bashi amsaba, sai kuma can daga baya ya amsa masa.

Amma dai Magana mafi inganci ita ce Mu’awiya ne ya fara aika masa wasika, sannan ya mayar masa da sharudda. Mu’awiya yayi haka ne saboda tsron kasa Irakawan da ya yaudara su canza ra’ayinsu. Su sake komawa wajen Imam Al-Hassan (a) a kuma shiga yaki. Don ya san cewa idan Imam Al-Hassan (a) ya sami mayaka isassu zai shiga yaki da shi. Dun haka tun lokaci bai kure masa ba, ya gabatar da bukatar Sulhu da Imam Al-Hassan (a) don tabbatar da cewa ba’a yi yaki ba.

Kuma zamu fahinci haka ne daga khudubar Imam Al-Hassan (a) a Mada’in inda yake cewa {Mu’awiya ya kir ani zuwa wani al-amari wanda babu daukaka a cikinsa kuma babu adalci..}.

Sai dai abu mai muhimmanci shi ne, idan Imam (a) ne fara neman sulhu, hakkinsa ne, saboda jarrabawa mai tsanani da ya shiga, idan kuma Mu’awiya ne ya fara, sannan ya amsa shi ba babu wata matsala idan ya amsa masa.

Amma abu mai muhimmanci shi ne, ainihan sharuddan. Malaman tarihi sun yi sabani a cikin aininhin sharuddan sulhun. Ga kuma wasu daga cikinsu.

01-Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa, Imam Al-Hassan ya aiki jakadu biyu zuwa wajen Mu’awiya, kuma su ne Amru dan Salmatah Al-Hamedani, da Muhammad dan Ashash Alkindi, su je su tabbatar da gaskiyan mu’awiya na bukatar sulhuntawa su kuma san me yake so da sulhun. Sai Mu’awiya ya basu wannan wasikar da zamu kawo.

Da sunan Allah Mai Rahama mai Jinkai

Wannan wasikar ta Al-Hassan dan Aliyu ne daga Mu’awiya dan Abusufyan, Lalle na sulhunta da kai kan cewa al-amarin shugabanci zai koma gareka a bayana, a kan haka in ana dauki alkawali daga Allah da kuma da manzonsa Muhammad, ina daukan al-kawali mafi girma daga Allah, alkawalin da wanda yafi tsanani da wani zai dauka daga Allah.

Ba zana neman cutar da kai ba ko isar da wata cutarwa gareka, sannan na yi alkawalin zan baki dirhami miliyon guda a ko wace shekara daga Baitul malin musulmi. Sannan na yi alkawalin baka, harajin Fasaa da kuma Doro Bajir wadanda zaka iya aika ma’aikatanka zuwa can. Kuma aikata abinda kaga dama a can. Kuma Abdullahi dan Amir da Amru dan Salmatah Alkindi, da Amdullahi dan Samratah da Muhammad dan Ashash Alkindi sune shaida. An rubuta ta a cikin watan Rabi’un Thani shekara ta 41 bayan hijira.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted