A jiya Juma’a ne Mahukunta a kasar DRC sun ce, mutane fiye da 200 sun kwanta dama sanadiyar ruftawar wani ramin hako ma’adanin “Coltan”dake gabashin kasar.
Sanarwar ta ce, an sami afkuwar hatsarin ne a ranar Larabar da ta gabata, sai dai ba a iya samun cikakken adadin mutanen da su ka rasu ba sai a jiya Juma’a.
Wurin hako ma’adanin da lamarin a faru shi ne Robaya wanda yake kunshe da kaso 15% da dukkanin ma’adanin “Coltan” da ake da shi a duniya. Kamfanonin da suke kera wayoyin hannu da kuma na’ura mai kwakwalwa suna amfani da shi a kere-kerensu.
Wani jami’in gwamnati ya fada wa manema labaru cewa; alkalumma sun tabbatar da cewa wadanda su ka rasa rayukan nasu, sun kai 227, sun kuma hada mata da kananan yara.
Gabashin DRC dai yana cike da ma’adanan da Allah ya shimfida kwance a karkashin kasa, da wasu daga cikinsu su ne mafi yawa da ake da su a duniya.
Kasashen duniya masu manyan masana’antu suna gogoriyon samun kaso mafi tsoka na wadannan ma’adanan na DRC.