Jami’an Gwamnatin Iran Sun Ci Gaba Da Maida Martani Ga Tarayyar Turai Dangane Da IRGC

Manya-manyan Jami’an gwamnatin JMI sun ci gaba da maida martani ga kungiyar tarayyar Turai wacce ta kira dakarun juyin juya halin musulunci  na kasar Iran

Manya-manyan Jami’an gwamnatin JMI sun ci gaba da maida martani ga kungiyar tarayyar Turai wacce ta kira dakarun juyin juya halin musulunci  na kasar Iran wato IRGC kan cewa yan ta’adda ne.

Kamfanin dillancin labaran ISANA na kasar Iran ya nakalto Dr Ali Larijani sakatarin majalisar koli ta tsaron kasar Iran yana fadar haka. Dr Larijani ya kara da cewa  wasu kasashen da suke kiran dakarun kare juyin juya halin muslunci a matsayin dakarun ‘yan ta’adda a wajen Iran sune yan ta’adda na gaskiya a wajen Iran. Sannan da sannu zasu girbi abinda suka shuka da wannan matakin da suka dauka a kan IRGC.

Larijani ya bayyana haka ne a yau Jumma’a a shafinsa ta zumunta na X, a lokacinda yake maida martani ga kasashen turai kan matakin da suka dauka a kan dakarun na IRGC. Ya kara da cewa, duka cutarwa da ta sami dakarun IRGC daga sojojin wadan nan kasashen Turai, Iran zata maida martani a kan sojojinsu.

Sai kuma kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf yana cewa, dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran IRGC sune rundurar sojojin kasar Iran mafi karfi  a kasar Iran, kuma sun yi fice wajen yakin da yan ta’adda ba a cikin kasar kadai ba, hata a yankin kudancin Asia sun taka rawa mai kyau wajen yakar yan ta’adda. Qalibaf ya kammala da cewa, wadanda suke tare da yan ta’adda ne kawai suke iya kiransu yan ta’adda kamar yadda zamu fahinci haka a yankin.

Sai kuma alkalin alkalan kasar Iran Hujjatul Islam Mohsen Ejei, wanda yake cewa kasashen turai sun sanya dakarun IRGC a cikin kungiyoyin yan ta’adda a wajensu, amma a wajen sauran kasashen duniya kuma sune a gaba gaba wajen yaki da ayyukan ta’addanci. Shahid Janar Qasim Sulaimani ne ya jagoranci yaki da kungiyoyin yan ta’adda wadanda Amurka da Turai suka samar shekaru kimani 15 da suka gabata a kasashen Siriya da Iraki kuma ya sami nasara a kansu. Sakamankon haka ne Donal Trump na kasar Amurka ya kasheshi don ya bata masu shirinsu.

Don haka ba abin mamaki ne ba, idan kungiyar EU ta zayyana IRGC cikin kungiyoyin yan ta’adda saboda su ne suke samar da yan ta’addan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted