Ministocin harkokin wajen kasashen Iran da turkiyya sun hadu a birnin Istambul na kasar Turkiyya a safiyar yau Jumma’a kuma sun tattauna al-amura wadanda suka shafi kasashen biyu da kuma matsalolin tsaron da ake fuskan a yankin.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa, ziyarar Abbas Aragchi zuwa kasar Turkiyya a wannan karon yana da matukar muhimmanci saboda irin halin da yankin yammacin Asia take ciki.
A jawabin bayan taron da Abbas Aragchi yayi da tokwaransa na kasar Turkiya Hakan Fidan sun bayyana anniyar kasashen biyu ta aiki tare don karfafa dankon zumuncin da ke tsakaninsu.
Sun kuma bayyana matsalolin tsaron da ake fuskanta a yankin a halin yanzu suna da matukan hatsari, don haka akwai bukatar kasashen yankin musamman Iran da Turkiyya su tuntubi juna don sanin mafita daga halin da ake ciki a yankin.
Haduwar ministocin na zuwa ne a dai dai lokacinda ake zaman jiran yakin da Amurka zata kaiwa JMI da nufin tumbuke gwamnatin JMI wacce aka kafa kimani rabin karnin da ya gabata.
Wannan bayan da Amurkla da kasashen yamma tare da HKI suke yi duk abinda zasu iya yi tun kafa JMI na kifar da gwamnatin amma suka kasa. Daga cikin har da takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kasar da kuma yaki kai tsaye na kwanaki 12 a cikin watan yinin da ya gabata.