Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro da sauransu, da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.
/////…. Madallah, masu sauraro shirimmu nay au zai fara da labarin, sojojin Iran, majiyar sojojin kasar ta bada sanarwan mikawa Sojojin Kasar KarinJiragen Yaki Wadanda Ake Sarrafasu Daga Nesa Har Guda 1000.
Sojojin kasar Iran sun karbi karin jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa ko Drones dubu guda don karfafa sojojin kasar ta sama da kasa da kuma ruwa.
Wannan yana daga cikin shirin kasar na karfafa karfin sojojin kasar na makaman zamani, wanda yafi dacewa da a irin wannan yakin.
Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa, jirgin yaki mai dakon jiragen sama Armada ya kama hanya zuwa yankin tekun farisa sannan washinton tana kallon duk abinda Iran take yi, banda haka ya kara da cewa farmaki kan kasar yana daga cikin zabin da yake da shi.
Sai dai gwamnatin kasar Iran ta kara jaddada cewa a shirye take ta maida martani mai tsanani kan wanda ya takaleta da yaki. Duk da cewa kofar diblomasiyya mai ma’ana a bude take.
Major General Amir Hatami yace sojojin kasar sun ware wasu makamai masu muhimmanci don amfani da su a duk yakin da zai iya tasowa tsakanin kasar Iran da Amurka da kuma kawayenta na kusa da nesa.
02-Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran bata adawa da hanyar diblomasiyya, amma dole ne ta kasance ta bangarori biyu masu yenci, da kuma mutunta juna.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin majalisar dokokin kasar Iran yana fadar haka a hirar da ta hada shi da tashar talabijan ta CNN wanda aka watsa a yau Alhamis. Ya kuma kara da cewa, ya zuwa yanzu shugaban kasar Amurka Donal Trump ya tabbatar da cewa shi yana son ya fada kuma a bi kawai, idan ba haka ba zai yi amfani da karfi don cimma manufofinsa a kan kasar Iran.
Qalibaf ya ce a cikin watan yunin shekarar da ta gabata, kasashen biyu suna cikin tattaunawa Amurka da HKI suka kaiwa kasar hare-hare, wanda ya nuna yaudara da kha’inci a fili. Babban jami’in siyasa na kasar ta Iran ya kammala da cewa, Iran ba zata amince da karban umurni daga kasar Amurka ba zata amince da kama karya ba. Saboda an kafa kasar saboda rashin amincewa da hakan.
Yace idan Trump yana neman zaman lafiya to kuwa ya san hanyar, idan kuma ba haka ba, to kuwa Iran ba zata jada baya a matsayinta na kasa mai cikekken yenci ba.
03-Aragchi: Sojojin Iran Sun Dora Yatsunsu A Kan Kunamar Makamansu
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, sojojin Iran sun rika sun dora hannayensu kan kunamun makamansu, suna jiran duk wanda zai takaleta da yaki.
Kamfanin dillancin labaran IRANa na kasar Iran ya nakalto ministan a yau Alhamis yana maida martani ga shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda yake kara jaddada shirinsa na farwa kasar sa da yaki.
Yace: Sojojimmu a shirye suke, kuma tuni sun dora hannayensu kan kunamun makamansu, don maida marta mai karfi kuma mai zafi kan duk wanda ya farwa kasar da yaki, daga sama kasa ko ruwa.
Aragchi ya kara da cewa yakin kwanaki 12 da ya gabata, ya sa mun dauki darasi wajen gaggawa daukar fansa da maida martani. Ministan ya maida martanin ne ga shugaban ne a jiya Laraba a kuma shafinsa na X.
Daga karshe ministan ya kammala da cewa, a dai dai lokacinda take wannan shirin yaki, kofar tattaunawa ta mutuinta juna a bude take, a kan shirinta na makamashin nukliya wanda zai bawa JMI hakkinta na sarrafa makamashin nukliya ta zaman lafiya. Yace Iran bata neman mallakar makaman Nukliya. Yace irin wadan nan makaman basa daga cikin shirimmu na tsaron kasa.
04-Tarayyar Turai Ta Dorawa JMI Sabbin Takunkuman Tattalin Arziki
Kungiyar tarayyar Turai EU ta kakabawa JMI sabbin takunkuman tattalin arziki don abinda ta kira murkushe masu zanga-zanga.
Tashar talabijan ta Almayadeentv ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar majalisar ministocin harkokin waje na tarayyar tana fadar cewa, takunkuman a wannan karon suna nufin daddaikun mutane ne da kuma wasu ma’aikatu wadanda wai suke da hannu wajen murkushe zanga-zangar masu adawa da gwamnatin kasar a cikin yan makonni da suka gabata.
Labarin ya kara da cewa, banda murkushe yan ta’adda da suke kira masu zanga zanga, iran dana da hannu wajen taimakawa kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine kimani shekaru 3 da suka gabata.
Banda haka ministocin sun kara da cewa nan ba da dadewa ba zasu amince da wata doka wacce zata sanya dakarun kare juyin juya halin musulunci a kasar wato IRGC a matsayin kungiyar yan ta’adda a wajensu.
Kafin haka dai wadan nan kasashe da Amurka da kuma HKI sun turo yan ta’adda daukeda makamai zuwa cikin kasar Iran don rikita kasar sannan da hare-hare su biyo baya. Sannan a maida martani ministan harkokin wajen kasar Iran Araghchi yace: EU ta tafka “babban kuskure” kan ayyana IRGC ‘yan ta’adda
Ministan Harkokin Wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya mayar da martani mai karfi ga matakin da Tarayyar Turai ta dauka kan Iran, ciki har da sanya dakarun kare juyin juya halin musulinci na Iran a matsayin “kungiyar ‘yan ta’adda.
” A cikin wani sako da aka wallafa a shafin sada zumunta na X, Araghchi ya yi Allah wadai da wannan mataki da ya danganta da “babban kuskure na dabaru.”
Araghchi ya jaddada cewa, a halin da ake ciki na karuwar tashin hankali a yankin, kasashe da dama suna aiki tukuru don hana barkewar yaki gaba daya a Gabas ta Tsakiya, amma babu ko daya daga cikin kasashen Turan”
A cewar ministan harkokin wajen Iran, Turai ta dauki wani mummunan matsayi ta hanyar bayar da gudummawa ga tabarbarewar yanayin da ake ciki.
Araghchi ya kuma yi Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin munafunci bayyananne na tsarin Turai.
Ya soki rashin daukar matakin Turai a kan laifukan da gwamnatin Isra’ila ta aikata a Gaza, yayin da ya nuna saurin da wasu jami’an Turai ke ikirarin kare hakkin dan adam idan ana maganar Iran.
Ga ministan, wannan ra’ayi na son zuciya wani kamfen ne na farfaganda da aka tsara don boye raguwar tasirin Turai da rawar siyasa a fagen kasa da kasa.
05-Limamin Tahran: Amurka Ba Za Iya Maimaita Abinda Ta Sha Kashi Akansa A Iran Ba
Wanda ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran Hujjatul Islam Sayyid Muhammad Hassan Abu Turabi ya ce; Amurka ba ta isa ta maimaita kuskure da ta yi akan Iran a baya ba.
Limamin na Tehran ya yi Ishara da yadda kasashen turai su ka shelanta rundunar kare juyi ( IRGC) a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda, yana mai cewa matakin nasu babu hankali a ciki, domin aikin da IRGC suke yi, shi ne fada da ta’addanci da ‘yan ta’adda.
Haka nan kuma ya ce; matakin na tarayyar turai ba komai ba ne, sai keta dokokin kasa da kasa, domin al’ummar Iran sun dauki rabin karni suna fada da ayyukan ta’addanci daga ciki har da kungiyar Da’esh.
06-Gaza: Sojojin Mamaya Sun Ci Gaba Da Kisa Da Kuma Killace Yankin
Sojojin HKI sun ci gaba da kisa tare da killace zirin Gaza, a dai dai lokacinda ake cika kwanaki 111 da tsagaita wuta tsakanin yahudawan da kuma Falasdinawa.
Tashar talabijan ta Almayadeentv ta kasar Lebanon ta bayyana cewa a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata kadai sojojin yahudawan sahyoniyya sun keta hurumin yarjeniyar tsagaita wutan a yankunan Gaza daban daban.
Labarin ya kara da cewa a safiyar ranar Alhamis sojojin mamayar sun kai hari kan gidajen falasdinawa birnin Rafah dake kudancin Gaza. Haka ma tankunan yakin yahudawan sun bude wuta kusa da Mauraaq daga arewacin Rafah.
Har’ila yau tankunan yakin yahudawa sun yi barin wuta mai yawa a gabacin birnin Khan Yunus daga kudanci yankin. A tsakiyar Gaza kuma sojojin yahudawan sun yi barin wuta kan gabacin sansanin yan gudun hijira na Al-Buraij.
Labarin ya kara da cewa tun bayan shelanta tsagaita wuta a gaza a ranar 11 ga watan Octoban shekarar da ta gabata, yawan falasdinawan da yahudawan suka kashe ya kai 492, sannan wadanda suka ji rauni kuma sun kai 1,356 sannan shahidan da aka zakulo daga burbushin gine-ginen da aka rusa zuwa 715. Wannan bisa kididdigan ma’aikatar lafiya na gaza.
Wannan kuma ya kara adadin falasdinawa da suka yi shahada tun fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 zuwa dubu 71,667 wadanda suka ji rauni kuma zuwa dubu 171 343.