An bude taron kasa da kasa akan makamashi mai tsafta, da kuma muhalli wanda ya sami halartar tawagogi daga kasashe mabanbanta.
Daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a wurin taron sun hada da yadda za a samar da makamashi mai tsafta da kuma yadda za a kare muhalli da kawo karshen gurbata shi a nan gaba.
Mai bai wa Fira Ministan kasar Iraki shawara akan harkokin muhalli Dr. Ali al-Lami ya jaddada cewa; Muhimmiyar manufar wannan taron dai shi ne taimakawa kasar Iraki ta sauya salon yadda take amfani da makamashi na man fetur da dangoginsa, zuwa makamashin da ba ya gurbata muhalli. Haka nan kuma ya ce, cimma wannan manufa yana bukatar rage yawan man fetur da dangoginsa da ake amfani da shi da zai rage gurbata muhalli.
Wani kwararre a fagen makamashi Ra’id al-Shaikhali ya yi Ishara da cewa; Iraki tana da damar da za ta iya tashi zuwa mai amfani da makamashi mai tsafta, sai dai har yanzu ba a isa wurin ba.
Haka nan kuma ya yi Magana akan yadda ya zama wajibi ayi aiki a tsakanin kasashe a fagen samar da makamashi mai tsafta, da rage amfani da makamashin da yake gurbata muhalli.