Araghchi : EU ta tafka “babban kuskure” kan ayyana IRGC ‘yan ta’adda  

Ministan Harkokin Wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya mayar da martani mai karfi ga matakin da Tarayyar Turai ta dauka kan Iran, ciki har da

Ministan Harkokin Wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya mayar da martani mai karfi ga matakin da Tarayyar Turai ta dauka kan Iran, ciki har da sanya dakarun kare juyin juya halin musulinci na Iran a matsayin “kungiyar ‘yan ta’adda.

” A cikin wani sako da aka wallafa a shafin sada zumunta na X, Araghchi ya yi Allah wadai da wannan mataki da ya danganta da “babban kuskure na dabaru.”

Araghchi ya jaddada cewa, a halin da ake ciki na karuwar tashin hankali a yankin, kasashe da dama suna aiki tukuru don hana barkewar yaki gaba daya a Gabas ta Tsakiya, amma babu ko daya daga cikin kasashen Turan”

A cewar ministan harkokin wajen Iran, Turai ta dauki wani mummunan matsayi ta hanyar bayar da gudummawa ga tabarbarewar yanayin da ake ciki.

Araghchi ya kuma yi Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin munafunci bayyananne na tsarin Turai.

Ya soki rashin daukar matakin Turai a kan laifukan da gwamnatin Isra’ila ta aikata a Gaza, yayin da ya nuna saurin da wasu jami’an Turai ke ikirarin kare hakkin dan adam idan ana maganar Iran.

 Ga ministan, wannan ra’ayi na son zuciya wani kamfen ne na farfaganda da aka tsara don boye raguwar tasirin Turai da rawar siyasa a fagen kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted