Sojojin Mamaya Suna Ci Gaba Da Kisa Da Kuma Killace Yankin Gaza

Sojojin HKI sun ci gaba da kisa tare da killace zirin Gaza, a dai dai lokacinda ake cika kwanaki 111 da tsagaita wuta tsakanin yahudawan

Sojojin HKI sun ci gaba da kisa tare da killace zirin Gaza, a dai dai lokacinda ake cika kwanaki 111 da tsagaita wuta tsakanin yahudawan da kuma Falasdinawa.

Tashar talabijan ta Almayadeentv ta kasar Lebanon ta bayyana cewa a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata kadai sojojin yahudawan sahyoniyya sun  keta hurumin yarjeniyar tsagaita wutan a yankunan Gaza daban daban.

Labarin ya kara da cewa a safiyar ranar Alhamis sojojin mamayar sun kai hari kan gidajen falasdinawa birnin Rafah dake kudancin Gaza. Haka ma tankunan yakin yahudawan sun bude wuta kusa da Mauraaq daga arewacin Rafah.

Har’ila yau tankunan yakin yahudawa sun yi barin wuta mai yawa a gabacin birnin Khan Yunus daga kudanci yankin. A tsakiyar Gaza kuma sojojin yahudawan sun yi barin wuta kan gabacin sansanin yan gudun hijira na Al-Buraij.

Labarin ya kara da cewa tun bayan shelanta tsagaita wuta a gaza a ranar 11 ga watan Octoban shekarar da ta gabata, yawan falasdinawan da yahudawan suka kashe ya kai 492, sannan wadanda suka ji rauni kuma sun kai 1,356 sannan shahidan da aka zakulo daga burbushin gine-ginen da aka rusa zuwa 715. Wannan bisa kididdigan ma’aikatar lafiya na gaza.

Wannan kuma ya kara adadin falasdinawa da suka yi shahada tun fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 zuwa dubu 71,667 wadanda suka ji rauni kuma zuwa dubu 171 343.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted