Kungiyar tarayyar Turai EU ta kakabawa JMI sabbin takunkuman tattalin arziki don abinda ta kira murkushe masu zanga-zanga.
Tashar talabijan ta Almayadeentv ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar majalisar ministocin harkokin waje na tarayyar tana fadar cewa, takunkuman a wannan karon suna nufin daddaikun mutane ne da kuma wasu ma’aikatu wadanda wai suke da hannu wajen murkushe zanga-zangar masu adawa da gwamnatin kasar a cikin yan makonni da suka gabata.
Labarin ya kara da cewa, banda murkushe yan ta’adda da suke kira masu zanga zanga, iran dana da hannu wajen taimakawa kasar Rasha a yakin da take fafatawa da kasar Ukraine kimani shekaru 3 da suka gabata.
Banda haka ministocin sun kara da cewa nan ba da dadewa ba zasu amince da wata doka wacce zata sanya dakarun kare juyin juya halin musulunci a kasar wato IRGC a matsayin kungiyar yan ta’adda a wajensu.
Kafin haka dai wadan nan kasashe da Amurka da kuma HKI sun turo yan ta’adda daukeda makamai zuwa cikin kasar Iran don rikita kasar sannan da hare-hare su biyo baya.