An Kai Wa Yar Majalisar Amurka Ilhan Umar Hari A Lokacin Zanga-zanga A Minnepolis

rahotanni sun bayyana cewa an kai hari kan ilhan umar yar majalisar Amurka lokacin da aka wurga mata wani abu da ba’a san ko menene

rahotanni sun bayyana cewa an kai hari kan ilhan umar yar majalisar Amurka lokacin da aka wurga mata wani abu da ba’a san ko menene ba a lokacin wani gangami a zauren garin  Minneapolis, inda take kira da a dakatar da ayyukan hukumar shige da fice a Minnesota,

wannan lamarin da ya faru yana nuna irin sabanin da ake da shi game da manufofin shige da fice da kuma tattaunawar siyasa musamman ga fitattun yan siyasar Amurka kar irin su ihan umar

a matsayinta na wadda ke kan gaba wajen fafutukar kare hakkin baki  yasa take fuskantar suka sosai, wanda ke nuna rarrbuwar kai tsakanin alumma game da hukumar shige da fice a kasar Amurka.

ilhan omar tana kira ne da a kawo karshen mataken da ake dauka na aiwatar da dokar shige da fice a Minnesota a lokacin da aka kai harin kuma ta jadda bukatar da ake da ita na sanya tausayi a tsarin dokar ta jami’an shige da fice.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted