“Yan Sandan Habasha Sun Kama Mutane 22 Masu Alaka Da Fataucin Mutane

Jami’an ‘yan sandan kasar Habasha sun kama  wasu mutane 22 da suke da alaka da fataucin mutane kusan 2,000 wadanda kuma su ka haddasa mutuwar

Jami’an ‘yan sandan kasar Habasha sun kama  wasu mutane 22 da suke da alaka da fataucin mutane kusan 2,000 wadanda kuma su ka haddasa mutuwar mutane biyu.

Sanarwar da ‘yan sandan kasar ta Habasha su ka fitar ta kuma ce,mutanen da aka kama suna a cikin wata kungiya ce mai samun miliyoyin kudade ta hanyar fataucin mutane da kuma yin garkuwa da su.

Masu hijirar da ta saba doka dai suna ratsawa ta kasar Habasha daga can su nufi ruwa, sannan su shiga turai. Kungiyoyin da suke fatauncin mutane suna amfani da wannan bukatar  ta mutane domin yaudararsu da karbar musu kudade.

Mahukuntan kasar ta Habasha sun ce, kungiyar ta masu laifi suna yaudarar ‘yan hijira da yi musu alkawulla na karya akan cewa za su sami kyakkyawar rayuwa a cikin kasashen turai, bayan sun ratsa kasar Libya.

Sai dai maimakon a kai su turai din sai a tsare su a cikin wasu manyan dakunan adana kaya da tilasata su tuntubar danginsu da ‘yan’uwansu akan su aiko da kudade, ba kuma za su saki wadannan mutanen ba har sai sun karbi kudi.

Sanarwar ta kuma ce, wadannan mutanen da aka kama, sun karbi kudaden da sun kai Birr biliyan 2.16, da ya kai dalar Amurka miliyan 13 daga hannun wadannan ‘yan hijirar da su ka yi garkuwa da su, da sun  kai 1,800.

Biyu daga cikin mutanen sun rasa rayukansu, yayin da wasu 15 su ka bace. A cikin watan Ogusta, an yanke wa wasu mutane 5 hukuncin saboda fataucin mutane.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted