Shugaba Erdogan na Turkiyya da takwaransa na Najeriya Bola Tinubu sun jagoranci sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama a tsakanin kasashen biyu.
Matakin ya shafi zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban-daban na masana’antu, kasuwanci, zuba jari, tsaro da dai saurensu.
An sanya hannu kan yarjejeniyoyi tara jimilla a gaban Shugaba Recep Tayyip Erdogan da Tinubu bayan tarurrukan hadin gwiwa a Ankara.
Yarjejeniyar ta kunshi horar da sojoji, samar da tsaro, manufofin kasashen waje, kafofin watsa labarai da sadarwa, manyan makarantu, shaidar amincewa da ingancin abincin halal, horar da jamiāan diflomasiyya, da harkokin zamantakewa da inganta rayuwar mata.
Tinubu ya ce Nijeriya na da niyyar zurfafa hadin gwiwa da Turkiyya, musamman a fannin tsaro da cinikayya, yana mai ambaton kokarin da aka yi na yaki da rashin zaman lafiya da habaka ci-gaban tattalin arziki.
Cinikayya tsakanin kasashen biyu ta kai dala miliyan 688.4 a cikin watanni 11 na farko na shekarar 2025.