Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar dinkin Duniya ta ce sama da mutane miliyan 3 da yakin da aka shafe kusan shekaru 3 ana gwabzawa a Sudan ne suka koma gidajensu, duk da yadda ake ci gaba da fuskantar mummunan rikici a sassan kasar.
A cikin wani rahoto da ta fitar , Hukumar ta ce Mutane Kimanin miliyan 3 da dubu 300, wadanda suka tsere sakamakon yakin ne suka komo gida tun daga watan Nuwamba shekarar da ta gabata.
Tun a watan Afrilun shekarar 2023 ne Sudan ta fada yaki, biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun kai daukin gaggawa na RSF.
Yakin ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane kuma ya haddasa abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin matsalar jinkai mafi girma a duniya, bayan da ya tarwatsa mutane kimanin miliyan 14 a ciki da wajen kasar.