Ministan leken asiri na kasar Iran ya bayyana cewa hadin kan mutanen kasar Iran yak are kasar daga barazanar da makiya sukewa kasar.
Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto Sayyid Esma’il Khatib ministan ayyukan leken asiri na JMI yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a wani taro a nan Tehran a yau Talata.
Khatib ya kara da cewa matukar kan mutanen Iran a hade yake, babu wata barazana da zata cutar da kasar. Ministan yana maganar yadda miliyoyin mutanen kasar Iran suka fito a ranar 12 ga watan Jeneru don nuna goyon bayansu ga gwamnatin musulunci ta kasar.
Ministan yayi tir da shirin kasashen yamma da HKI na rikita al-amura a cikin kasar ya kuma kara da cewa, Iran ta sha fuskantan ayyukan ta’addanci daban daban a cikin kasar wadanda HKI da kuma kasashen yamma karkashin Amurka suke goyon baya. Amma tare da taimakon Allah da kuma hadin kan da mutanen kasar Iran suke da shi dukkan makirce-makircensu sun lalace.
Yace wadan nan kasashe sun yi aiki na shekaru fiye da 40 don ganin bayan JMI amma sun kasa yin haka.
Ministan ya kammala cewa duk tare da matsin lamba da kuma takurawa na makiya mutanen kasar Iran sun ki bada dama wa makiya su rarraba mutanen kasar.