Sama Da Bakin-haure 50 Ne Suka Bace Bayan Nutsewar Jirginsu A Tekun Mediterranea

An ceto mutum guda a yayin da ake fargabar wasu mutane 50 sun salwanta a ruwa, bayan da wani kwale-kwale dauke da bakin-haure ya nutse 

Jirgin ruwa

An ceto mutum guda a yayin da ake fargabar wasu mutane 50 sun salwanta a ruwa, bayan da wani kwale-kwale dauke da bakin-haure ya nutse  a tekun  Mediterranean, kamar yadda mahukunta suka bayyana yadda lamarin ya afku

Mutumin, wanda ya kasance a cikin tekun tsawon sa’o’i 24 gabanin ceto shi, ya ce ya yi imanin dukkannin mutanen da ke cikin kwale-kwalen sun mutu, kamar yadda kungiyar agaji ta Alarm Phone, wadda ke aikewa da sakonnin kar ta kwana ga yan gudun hijira.

Wani jirgin ‘yan kasuwa ne ya ceto wannan mutumin a gabar ruwar Tunisia, kana ya kai shi Malta domin a duba lafiyarsa, kamar yadda rundunar sojin Malta ta bayyana.

sai dai Ƙungiyar Alarm Phone ba ta bayyana ranar da aka ceto mutumin daga teku ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted