Iran: An kama makamai 60,000 a wani samame cibiyar ‘yan ta’adda mai alaka da Mossad  

Jami’an tsaron Iran sun sanar da gano tarin makamai 60,000 da aka yi niyyar kai hare-haren ta’addanci dasu a Tehran An gano tarin makamman ne

Jami’an tsaron Iran sun sanar da gano tarin makamai 60,000 da aka yi niyyar kai hare-haren ta’addanci dasu a Tehran

An gano tarin makamman ne a wani samame a wata cibiyar kungiyar ‘yan ta’adda da Mossad ta horar wanda akayi niyyar amfani dasu a tashin hankalin kwanan nan don kai hare-hare masu muni yayin da zanga-zangar da ta rikide ta koma tashin hankali a kasar.

A halin yanzu, jami’an leken asiri sun gano tare da kama membobin wata “kungiyar ‘yan ta’adda mai haɗari” da aka ɗora wa alhakin kashe fararen hula.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Tasnim, wannan kungiyar, wacce Mossad ta horar a fannin dabarun yaki, an ba ta aikin amfani da rikicin don aiwatar da kisan kai.

An gano nau’ukan makamai daban-daban, ciki har da bindigogin AK-47 da harsasai, da kuma kayan sadarwa, kamar wayoyin dake aiki da tauraron dan adam.

An dai fara zanga-zangar lumana a Iran a kashen watan Disamba kafin daga bisani zanga zangar ta rikide zuwa tashin hankali saboda yadda kasashen waje suka rika ingiza masu zanga zangar ta hanyar nuna musu goyan baya da kuma shan alwashin kai musu dauki.

Masu zanga zangar sun kashe jami’an tsaro da fararen hula tare da lalata kadarorin jama’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted