Jagora: Muna Daukar Shugaban Kasar Amurka Mai Laifi

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Sayyid Ali Khmanei ya bayyana cewa; A wurinmu shugaban kasar Amurka mutum ne mai laifi. Jagoran juyin musulunci

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Sayyid Ali Khmanei ya bayyana cewa; A wurinmu shugaban kasar Amurka mutum ne mai laifi.

Jagoran juyin musulunci wanda ya gabatar da jawabi a ranar “Aiko Manzon Allah” da ita ce 27 ga watan Rajab, ya bayyana cewa; Al’ummar Iran suna daukar shugaban kasar Amurka a matsayin mutum mai aikata laifi saboda asarar da ya jawo musu da kuma karairayin da ya yi wa al’ummar ta Iran. Haka nan kuma jagoran juyin musulunci na Iran wanda ya karbi bakuncin mutane da dama a wannan rana ta “aiko manzon Allah” ya kuma yi Ishara da yadda aka kama mutanen da aka samu da laifukan aikata barna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted