Ministan Harkokin Waje Abbas Araghchi Ya Danganta tarzomar da ta barke a kasar kwanan Nan da Wani makircin Isra’ila don tada hankali da kuma niyyar kai sabon hari kan Jamhuriyar Musulunci.
Babban jami’in diflomasiyyar ya yi wannan tsokaci ne a wata hira ta musamman da tashar talabijin ta Amurka Fox News.
Da yake mayar da martani ga ikirarin da ake yi na yawan mace-mace a Iran, kamar yadda kafafen yada labarai na Amurka da Isra’ila da sauransu suka yada, Araghchi ya bada tabbaci cewa adadin wadanda suka mutu, a zahiri, ya kai daruruwan.
Ya bayyana cewa ‘yan ta’adda daga waje ne suka kara ta’azzara lamarin ta hanyar kai hare-hare kan jami’an tsaron Iran da fararen hula.
“Wadannan ‘yan ta’adda sun shiga zanga-zangar, suna amfani da ayyukan ta’addanci irin na Daesh.
Sun harbi jami’an ‘yan sanda, sun kona su da rai, sun yanke musu kai, sannan suka kai hari kan fararen hula,” in ji shi.
A tsawon kwanaki uku na farko, ba mu yi fada da masu zanga-zanga ba.
Jami’in ya ci gaba da da’awar cewa wadannan ‘yan ta’adda suna kokarin kara ta’addanci da gangan don kara yawan wadanda suka mutu don kokarin tabbatar da shigar kasashen waje cikin rikicin.
Domin Shugaban Amurka Trump ya riga ya bayyana cewa idan akwai kashe-kashe, zai dauki mataki. Manufarsu ita ce su jawo Amurka cikin wannan rikici,” in ji Araghchi. “Wannan makirci ne na Isra’ila da gangan.
A cewarsa a halin yanzu, Jamhuriyar Musulunci tana da cikakken iko kan yanayin tsaro a kasar, da kuma tarzomar da ta barke.