Iran ta bayyana sabbin takunkuman da Amurka ta kakaba mata a matsayin take hakkin bil adama.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Esmail Baqai, ya yi Allah wadai da sabbin takunkuman kan tattalin arziki da Amurka ta sanya wa abokan huldar Iran a ranar Laraba.
” Da yake fassara matakan Amurka na baya-bayan nan a matsayin ci gaban matsin lamba ta tattalin arziki, Esmail Baqai ya jaddada cewa al’ummar Iran sun fuskanci haramtattun takunkumai da matsin tattalin arziki tsawon sama da shekaru 75.
“Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kuma yi gargadi game da illolin da ayyukan Amurka na gefe daya da tilastawa ke yi wa tsarin ciniki na duniya, yana mai kira ga Majalisar Dinkin Duniya da cibiyoyinta, musamman Sakatare Janar, da su dauki nauyin da ke kansu na tabbatar da bin doka a duniya.
Sabbin takunkuman a cewar ma’aikatar Harkokin Wajen Iran nuna “kiyayya ce mai tsanani ga kasar” ta haifar da hakan.
Takunkuman na rashin ” tausayi” sun saba wa ka’idodin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa, inji Esmaeil Baghaei inda ya yi gargadin cewa takunkumin zai yi mummunan tasiri har a wajen iyakokin Iran, duba da yadda matakan Amurka na bangaranci ke wargaza tsarin ciniki na duniya gaba daya inji mai magana da yayun ma’;aikatar harkokin wajen kasar ta Iran.