A Uganda yau ne al’ummar kasar ke kada kuri’a a zaben shugaban kasar.
Masujefa kuri’a miliyan 21.6 ne aka kira zuwa rumfunan zabe a fadin kasar.
Shugaba mai ci Yoweri Museveni, wanda ya hau mulki a watan Janairun 1986, wato sama da shekaru arba’in da suka gabata, yana neman wa’adi na bakwai a kan ‘yan takara bakwai, ciki har da babban abokin hamayyarsa, madugun ‘yan adawa Bobi Wine.
Majalisar Dinkin Duniya da Amnesty International sun yi gargadi game da yanayi zaben yayin da gwamnati ta katse intanet.