Ministan Harkokin Wajen Iran Seyyed Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da shishigi na kasashen waje a cikin harkokin cikin gida na kasar.
Abbas Araghchi ya bayanna hakan ne a wata hira ta wayar tarho da takwaransa na Faransa, Jean-Noël Barrot, Inda suka tattauna kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da halin da ake ciki a yankin da ma duniya.
A yayin zantawar, bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan dangantakar da ke tsakanin kasashen, musamman a harkokin ofishin jakadancin.
Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya yi Allah wadai da shisshigin kasashen waje a harkokin cikin gida na kasar, yana mai nuni da abubuwan da suka faru kwanan nan a Iran inda zanga-zangar lumana ta koma tashin hankali kuma ‘yan ta’adda da aka horar da su daga kasashen waje sukayi amfani da damar wajen aikata mummunan barna, lamarin da ya haifar da asarar rayuka, lalata kadarori, da lalata kayayyakin more rayuwa na jama’a.
Ya yi kira da a yi Allah wadai da shisshigin kasashen waje kuma ya jaddada cewa Iran ba za ta lamunci duk wani keta ‘yancinta ba.
Ministan Harkokin Waje Abbas Araghchi ya bayyana tarzomar da aka yi kwanan nan da kuma ta kai wa Iran hari a matsayin ta’addanci da ya yi kama da na kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh, yana mai cewa hakan ya nuna ci gaba da yakin da Amurka da gwamnatin Isra’ila suka kaddamar wa Iran a watan Yuni.