Somaliya ta sanar cewa za ta soke dukkan yarjejeniyoyi da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Wannan matakin ya shafi ayyukan tattalin arziki da hadin gwiwar tsaro.
An ruwaito cewa Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi amfani da yankin Somaliya don taimakawa wani dan fafutuka daga Yemen tserewa daga kasarsa.
Bayanai sun ce an fitar da Aidarous al-Zubaidi, shugaban Majalisar Wucin Gadi ta Kudu a Yemen, fita daga kasar da ta fada cikin yakin basasa tun 2014.
An ruwaito cewa al-Zubaidi ya bar Yemen da jirgin ruwa, ya yi tafiya zuwa Somaliland, sannan ya hau jirgin sama a Mogadishu zuwa Abu Dhabi, ba tare da sanin hukumomin Somaliya ba.
Saidai a cikin sanarwa uku daban-daban, Somaliland, Puntland da Jubaaland sun nanata cewa gwamnatin tarayya a Mogadishu ba ta da “ikon” soke yarjejeniyoyin da aka yi da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Tun bayan da Isra’ila ta amince da yankin Somaliland a matsayin kas amai cin gashin kanta a karshen watan Disamba, rikici ya fara barkewa tsakanin Somaliland da Somaliya.