Gwamnatin kasar Iran ta kaddamar da bincike don gano yadda yan ta’adda suka kwace zanga-zangar lumana ta yan kasuwa wadanda suke bukatar a kyautata rayuwarsu suka maida ita tashe-tashen hankula da kuma kashe-kashe da kone-kone da kuma lalata dukiyoyin alummar kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin gwamnati Fatimah Muhajirani tana fadar haka a yau Talata ta kuma kara da cewa gwamnatin ta kaddamat da kwamiti don gudanar da bincike saboda mutane su san gaskiyar abinda ya faru.
Muhajirani ta kara da cewa katse yanar gizo ko internet da aka yi a cikin yan kwanakin da suka gabata, wani zabi ne don tsaron kasar, ba siyasa ba. Kuma gwamnatin Iran tana ganin hakkin mutanene su san abinda yake faruwa a cikin gwamnatinsu.
Ta nuna alhininta ga wadanda suka rasa rayukansu a rigima ta baya-bayan nan, kama daga Jami’an tsaro da kuma fararen hula.
A jiya Litinin ce miliyoyin mutanen Iran suka fito kan titunan a manya-manyan birane da garuruwan kasar, inda suka yi allawadai da yan ta’adda wadanda suka kashe mutanen kasar suka kuma kona dukiyoyinsu da sunan tsadar rayuwa, sannan da nuna goyon bayansu ga gwamnatin musulunci ta kasar.