Somalia Ta Bata Dukkan Yarjeniyoyi Tsakaninta Da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)

Gwamnatin kasar Somalia ta bada sanarwan bata dukkan yarjeniyoyi tsakaninta da hadaddiyar daular larabawa ko UAE tare da zarginta da zagon kasa ga hadin kan

Gwamnatin kasar Somalia ta bada sanarwan bata dukkan yarjeniyoyi tsakaninta da hadaddiyar daular larabawa ko UAE tare da zarginta da zagon kasa ga hadin kan kasar ta Somalia.

Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ ya nakalto majiyar gwamnatin kasar Somalia na fadar haka, ya kuma kara da cewa UAE tana zagon kasa ga diyauci, hadin kai da kuma daukakar kasar Somalia.

Kafin haka dai kasar UAE ta gina tashar Jiragen Ruwa, a ruwa mai zurfi a birnin Berbera. Sannan ta kulla wasu yarjeniyoyin da gwamnatin Somalia dangane da tashoshin jiragen ruwa na Bosaso, da Kismayo. Tace dukkan wadannan yarjeniyoyi sun tashi daga aiki.

A cikin watan da ya gabata ne HKI ta bada sanarwan amincewa da yankin Somaliland wanda yake son ballewa daga kasar Somalia. Saboda amfani da yankin don yakar kasashen musulmi da larabawan da suke yankin. Sannan gwamnatin Abudabi tana goyon bayan Haramtacciyar kasar kan wannan manufofinta.

Tun shekara ta 1991 ne yankin Somaliland ta shelanta ballewa daga kasar Somalia, amma babu wata kasa a duniya da ta amince da ita, sai HKI a cikin watan da ya gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted