Majalisar dinkin Duniya ta ce yan gudun hijirar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da ke Burundi sama da 53 sun mutu.
Hukumar kala da yan Gudun Hijira ta Majalisar dinkin duniya (UNHCR) ta shaidawa manema labarai cewa cikin adadin mutanen, 25 daga cikinsu sun mutu ne a sakamakon barkewar cutar amai da gudawa, yayin da wasu 6 suka mutu a sakamakon karancin Jini da sauran matsalolin da suka shafi rashin abinci mai gina jiki.
Majalisar dinkin duniya ta ce tana aiki tare da ma’aikatar lafiya da sauran abokan hulda domin binciko ainihin musabbabin mutuwar sauran mutanen.
Fiye da mutane 100,000 yan kasar Congo ne suka nemi mafaka a Burundi tun bayan da rikici ya barke a yankin kan iyaka da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, kuma mayakan suka kwace garin Uvira.
Jean Jacques Purusi, gwamnan lardin Kudancin Kivu inda garin Uvira yake, ya bayyana abin da ke faruwa a Burundi a matsayin tashin hankali, yana mai cewa wannan matsala ta shafi kowa a duniya.