Gwamnatin Tarayya ta gabatar da kudirin ware Naira biliyan 42.18 domin samar da muhimman kayayyakin kiwon lafiya ga ‘yan Nijeriya miliyan 10 da ake ganin suna da rauni sosai, a cikin kasafin kudin shekarar 2026 da aka gabatar wa Majalisar Tarayya.
Wannan kuɗin na daga cikin jimillar Naira tiriliyan 2.48 da aka ware wa bangaren kiwon lafiya a kasafin kuɗin shekarar, inda aka tanadi kudaden domin sayen magunguna, kayan amfani a asibitoci, kayayyakin aikin likitanci, sinadaran gwaje-gwaje da kayan gwajin cututtuka, don kulawa da lafiya musamman ga talakawa a faɗin kasar.
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya mika kudirin kasafin kuɗin shekara ta 2026 ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa a watan da ya gabata, inda ya bayyana muhimman abubuwan da gwamnatin sa ta ba fifiko a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tattalin arziki da zamantakewa.
A jawabinsa yayin gabatar da kasafin kudin, Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin bangarorin kiwon lafiya da ilimi wajen gina alumma, yana mai cewa babu wata kasa da za ta ci gaba fiye da ingancin mutanenta.