Sakataren Majalisar Tsaron Rasha Sergei Shoigu ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Litinin da Sakataren Majalisar Tsaron Koli ta Iran Ali Larijani, a cewar wata sanarwa daga ofishin manema labarai na Majalisar Tsaron Rasha.
Sanarwar ta nuna cewa Shoigu ya yi ta’aziyyar wadanda rikicin da ya faru kwanan nan a Iran ya shafa kuma ya yi Allah wadai da “wani yunƙuri na wasu daga waje na tsoma baki a harkokin cikin gidan Iran,” yana mai nuni da kalamai da tsoma baki na baya-bayan nan na Isra’ila da Amurka game da halin da ake ciki a Iran.
A yayin tattaunawar, Shoigu ya jaddada shirin Rasha na haɓaka haɗin gwiwa tsakaninta da Iran, bisa ga “Yarjejeniyar Haɗin gwiwa ta Dabaru Tsakanin Rasha da Iran,” wadda aka sanya wa hannu a ranar 17 ga Janairu, 2015.
Bangarorin biyu sun amince su ci gaba da tuntubar juna da daidaita matsayinsu don tabbatar da tsaro, wanda ke nuna aniyarsu ta ƙarfafa tsaro da haɗin gwiwa a cikin tsarin haɗin gwiwar da ke tsakanin ƙasashen biyu.