Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Syria ta sanar da kama wadanda su ka dasa bom a cikin masallacin Imam Ali ( a.s) na Mabiya mazhabar Ahlul Bayti ( a.s) a birnin Homs, tare kuma da wasu takardu na bayanai da suke tabbatar da cewa suna da hannu dumu-dumu a harin.
Jami’an tsaro a birnin Homs sun kai samamen hadin gwiwa da jam’an leken asiri da ya kai ga kamo Ali Ahmad Ata’ullah al-Diyab, da Anas al-zarad da dukkaninsu ‘yan kungiyar “Da’esh” ne.
A ranar 26 ga watan Disamba ne dai aka kai hari a masallacin Imam Ali Bin Abi Talib wanda ya yi sanadiyyar shahadar masu salla a cikinsa da kuma jikkata wasu.
Sanarwar mahukuntan kasar ta Syria ta ce, an yi nasarar kamo maharan ne bayan da aka gudanar da binciken kwakwaf akan kai da komowarsu da inda suke. An kuma same su da wasu abubuwan fashewa da makamai da albarusai, sai kuma wasu bayanai a wayoyi da suke tabbatar da cewa sun aikata wasu ayyukan ta’addancin.
Tuni aka mika mutanen biyu zuwa ga hukumar fada da ta’addanci domin ci gaba da gudanar da bincike akansu.
A ranar 26 ga watan Disamba ne dai aka kai wa masallacin Imam Ali ( a.s) hari wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 8 da kuma jikkata wasu 27 a yankin Wadiz-Zahab, dake Homs.