Bayanai daga Gaza na cewa har yanzu Zirin na fuskantar hare-hare daga gwamnatin mamaya ta Isra’ila.
Shaidu sun ba da rahoton cewa sojojin Isra’ila sun kai hare-hare ta sama, da kuma ruwan bama-bamai a yankuna da dama na Gaza, wanda hakan ke ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta wadda ta fara aiki tun daga ranar 10 ga Oktoba, 2025.
Jiragen yakin Isra’ila sun kai hari ta sama a kudu maso yammacin birnin Rafah da ke kudancin Gaza a ranar Lahadi, yayin da wani hari ta sama ya shafi yankunan gabashin sansanin ‘yan gudun hijira na Bureij da ke tsakiyar Gaza, in ji shaidu.
Jiragen yakin Isra’ila sun kuma yi luguden wuta a yankunan gabashin birnin Gaza, ciki har da unguwannin Tuffah da Zeitoun.
A arewacin Gaza, jiragen saman Isra’ila sun kai hare-hare ta sama da kuma rushe gine-gine da ke gabashin Jabalia da Beit Lahia, tare da harba manyan bindigogi, a cewar majiyoyin yankin.
Ba a samu rahoton asarar rayuka ba a hare-haren baya-bayan nan.
Tun daga watan Oktoban 2023, sojojin Isra’ila sun kashe mutane sama da 71,000, galibi mata da yara, tare da raunata wasu sama da 171,000 a cikin abin da aka bayyana a matsayin kisan kare dangi.
Duk da tsagaita wuta, hare-haren Isra’ila sun ci gaba, inda suka kashe Falasdinawa 425 tare da raunata wasu 1,189, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Gaza.