Kasar Turkiya Ta ce Isra’ila Ba Za ta Taba Cimma Hadafinta Ba A Kasar Iran

Ministan harkokin wajen kasar turkiya hakan fidan yayi mummunan suka ga isra’ila na taimakawa masu zanga-zanga da tada zaune tsaye a wasu birane a kasar

Ministan harkokin wajen kasar turkiya hakan fidan yayi mummunan suka ga isra’ila na taimakawa masu zanga-zanga da tada zaune tsaye a wasu birane a kasar iran, yace gwamnatin tel aviv hakarta ba za ta cimma ruwa ba kan kasar iran.

A wata hira da gidan talabijin din TRT yayi da shi ya fadi cewa makircin da isra’ila ke kullawa na haifar da rikici a kasar iran da dakile ci gaban da take samu ba zai yi nasara ba.

Da yake bayani game da dogon burin da prime ministan isra’ila banjemin na tanyaho da gwamnatinsa suke da shi na kifar da gwamnatin musulunci ta kasar iran, babban jami’in diplomasiyar yace kome yanzu afili yake don haka suna kuskuren lissafi kan irin mataken da alummar iran suke dauka.

Daga karshe ya tabo batun matsin lamba da mataken karya tattalin arziki da Amurka da kawayenta na yammacin duniya ke dauka kan iran, ya zarge su da sanya lamurran su zama masu wahalar gaske ta hanyar gabatar da wasu sharudda marasa tushe duk sanda iran ta zabi hanyar tattaunawa .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted