Amnesty International Ta Zargi Jami’an Tsaron Uganda Da Azabtar Da Mutane

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi jami’an tsaron Uganda da azabtar da mutane da kama su ba bisa ka’ida ba, yayin

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi jami’an tsaron Uganda da azabtar da mutane da kama su ba bisa ka’ida ba, yayin da kasar ke tunkarar zaben ranar 15 ga Janairu.

Shugaban kasar Yoweri Musebeni, mai shekara 81, na neman kara tsawaita mulkinsa na kusan shekaru 40, a daidai lokacin da ake zargin ana kara daukar tsauraran matakai domin murkushe ‘yan adawa.

Amnesty ta ce ta tattara shaidu da ke nuna jami’an tsaro na dukan masu zanga-zanga tare da harba hayakin mai sa  hawaye kan magoya bayan jam’iyyar adawa ta National Unity Platform, wadda Bobi Wine ke jagoranta.

Bobi Wine, tsohon mawaki da ya koma siyasa, ya taba kalubalantar Musebeni a zaben 2021, wanda aka yi ta takaddama kan sahihancinsa da kuma zargin amfani da karfin gwamnati wajen murda zaben.

Amnesty ta ce ta rubuta bayanan kama mutane kusan 400 daga cikin magoya bayan NUP a ‘yan watannin nan, inda da dama daga cikinsu suka bayyana cewa an doke su, an yi musu feshin barkonon tsohuwa, ko kuma an yi amfani da wutar lantarki a wajen azabtar da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted