Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya zargi gwamnatin Amurka da alhakin mayar da zanga-zangar lumana a Iran zuwa tashin hankali mai tsanani.
A cikin wata wasika da ya aike wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, Saeed Iravani ya ce Amurka ce ke da alhakin tashin hankali dake faruwa a Iran.
Ya yi Allah wadai da ayyukan gwamnatin Amurka da kuma hadin gwiwarta da gwamnatin Sahayonaya don tsoma baki a harkokin cikin gida na Iran.
Da yake Allah wadai da tsoma bakin Amurka ta hanyar barazana, tayar da hankali, manzon ya ce irin wadannan ayyukan da Amurka ke yi na wargaza zaman lafiya sun karya Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.
Kafin hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, sakatariyar Majalisar Koli ta Tsaron Kasa ta Iran ta ce gwamnatin Sahayoniya tana ci gaba da fafatawa da Iran bayan yakin kwanaki 12 a watan Yuni kuma ta canza dabarunta ne kawai tun daga lokacin.
Sanarwar ta kara da cewa kalaman da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kwanan nan sun bayyana wani makirci na hadin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila kan Iran, yana mai jaddada cewa al’ummar Iran, za ta sake dakile makircin makiya ta hanyar hadin kai da hadin kai.