Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Karbi Bakuncin Takwaransa Na Kasar Oman

Minsitan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Abbas Arakci, ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Oman, Badar al-Bu-Sa’idi, a yau Asabar a nan birnin Tehran.

Minsitan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Abbas Arakci, ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Oman, Badar al-Bu-Sa’idi, a yau Asabar a nan birnin Tehran.

Arakci ya karbi bakuncin Bu-Sa’idi ne a ginin ma’aikatar harkokin wajen Iran bayan da ya dawo daga ziyarar aikin da ya kai zuwa kasar Lebanon.

A jiya Juma’a ne dai ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana cewa, takwaran nasa na kasar Oman zai kawo Ziyara Iran.

Daga cikin muhimman batutuwan da bangarorin biyu su ka tattauna da akwai hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu da kuma tattauna abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin na yammacin Asiya.

 A yayin taron manema labaru da bangarorin biyu su ka gabatar sa’o’i, kadan da su ka gabata, ministan harkokin wajen Oman ya ce; Tehran da Muscat, suna aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya a cikin wannan yankin.

Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya ambato ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yana cewa; Ziyarar da bakon na Oman ya kawo tana nuni da zurfin alaka a tsakanin kasashen biyu.

Haka nan kuma ya ce; Da akwai alaka ta tarihi da al’ada mai tsawo a tsakanin kasashen biyu, sannan kuma ya kara da cewa: A halin yanzu kwararru a fagage da dama suna tattaunawa saboda daukaka wannan alakar.

Ya kuma kara da cewa; Bangarorin biyu sun daukarwa  kansu wajabcin ganin an sami zaman lafiya da tsaro a cikin wannan yankin.

Daga cikin batutuwan da bangarorin biyu su ka bijiro da su a yayin taron manema labarun da akwai falasdinu da wajabcin dakatar da kashe Falasdinawa da ‘yan sahayoniya suke yi.

Da yake amsa tambaya akan yadda haramtacciyar Kasar Israila ta yi furuci da yankin Somaliland a matsayin kasa mai ‘yanci, ministan harkokin wajen na Iran ya ce; Iran da Oman ba su yarda da batun ballewar yankin na Somaliland da kuma kasar Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted