Majalisar Dokokin Kasar Iran Sun Fara Taro Da Jami’an Tsaron Kasar A Asirce

Majalisar dokokin kasar Iran ta gudanar da taro na musamman kuma a asirce da manya-manyan jami’an tsaro da kuma jami’an gwamnatin wadanda suke kula da

Majalisar dokokin kasar Iran ta gudanar da taro na musamman kuma a asirce da manya-manyan jami’an tsaro da kuma jami’an gwamnatin wadanda suke kula da harkokin tattalin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa a safiyar Jiya Laraba ce aka gudanar da taron kuma sun tattauna dangane da halin da ake ciki a kasar a bangaren tattalin arziki da kuma tsaro a kasar.

Labarin ya kara da cewa kakakin majalisar dokokin kasar Mohammad Bakir Qalibaf ne ya jagoranci zaman, sannan shugaban yansandan kasar FARAJA Brigadier General Ahmadreza Radan, da ministan tattalin arziki da kudade Ali Madanizadeh da kuma ministan ayyukan noma Gholamreza Nouri Qezelje da kuma shugaban ofishin kasasfin kudi na kasa Hamid Poor-Muhammadi duk sun sami halattan taron.

A cikin yan makonnin da suka gabata, an yi ta samun tashe-tashen hankula a birane da dama a cikin kasar bayan faduwar darajar kudaden kasar idan an kwatanta da dalar aAmurka wanda ya jawo tashin farashin kayayyaki a kasuwannin kasar.

Takunkuman tattalin arziki mafi tsanani wadanda kasashen yamma suka dorawa JMI dai sun suna da tasiri a cikin halin da tattalin arzikin kasar Iran ta fada ciki.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted