Kungiyar Tarayyar Afirka ta bukaci Isra’ila ta janye amincewa da kasar Somaliland

Kwamitin siyasa, zaman lafiya da tsaro na kungiyar Tarayyar Afirka ya yi kira da a gaggauta janye amincewar da Isra’ila ta yi wa Somaliland. A

Kwamitin siyasa, zaman lafiya da tsaro na kungiyar Tarayyar Afirka ya yi kira da a gaggauta janye amincewar da Isra’ila ta yi wa Somaliland.

A wani sakon da ta wallafa a dandalinta na X bayan taron ministocin kungiyar Tarayyar Afirka, an bayyana cewa, “Majalisar Tarayyar Afirka ta yi Allah-wadai da kakkausar murya, kan amincewa da Isra’ila ta yi da abin da ake kira Jamhuriyar Somaliland.”

Ma’aikatar harkokin wajen Somaliya ta yi Allah wadai da ziyarar da ministan Isra’ila ya kai a birnin Hargeysa a ranar Talata don ganawa da jami’ai a Somaliland, inda ta bayyana cewa “ziyarar cin zarafi ce ga ‘yancin kai da kuma yankin Somaliya.”

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ce “duk wata Ziyara ko tuntuɓar juna, ko mu’amala da ke faruwa a cikin ƙasar Somaliya ba tare da izini daga gwamnatin tarayyar Somaliya ba, haramtacce ne, ba shi da halasci balantana amfani ko tasiri.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted