Kasar Uganda Ta Haramta Yada Duk Wani Gangami Kai Tsaye A kafafen Sadarwa

A dai dai lokacin da zabe ke ci gaba da karatowa a kasar Uganda gwamnatin kasar ta sanar da haramta yada zanga-zanga ko duk wani

A dai dai lokacin da zabe ke ci gaba da karatowa a kasar Uganda gwamnatin kasar ta sanar da haramta yada zanga-zanga ko duk wani gangami kai tsaye ta kafafen sada zumunta na zamani, a kokarin da shugaba Yoweri Museveni ke yi na neman sabon wa’adi don tsawaita mulkinsa na shekaru 40 a kasar ta gabashin Afrika

Tun kafin wannan zabe da zai gudana a ranar 15 ga watan da muke ciki, gwamnatin Uganda ta kame daruruwan magoya bayan ƴan adawa tare da daukar tsauraran matakai don kare duk wata barazana da aka iya faruwa.

Ma’aikatar sadarwa da fasaha ta Uganda ta fitar da sanarwar haramta yada duk wani gangami ko tarzoma ko rikici wanda ta ce yadasu kai tsaye ta kafafen sada zumunta zai haifar da tsoro a tsakanin jama’a gabanin babban zabe nan da kwanaki 10 masu zuwa.

Sai dai masu suka da kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce mahukuntan na Uganda sun sanya zanga-zangar yan adawa a matsayin tarzoma kuma suka bayyana tana tayar da rikici a tsakanin jama’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted