Iran ta kaddamarda ci gaba har guda 20 a fannin ilmin likitanci a jami’ar Shahid Beheshti dake nan Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa manya-manyan jami’an gwamnati a ma’aikatar kiwon lafiya ne suka jagoranci kaddamar da wadan nan ci gana da aka samu a bangaren cututtukan hakora da wasu bangarori, a sashen ilmin likitanci na Jami’ar.
Labarin ya kara da cewa dalibai da malaman sashen ilmin likitanci na jami’ar ne suka samar da wannan ci gaban a cikin gida ba tare da samun taimako daga wani daga waje ba. Wannan kuma ya kara tabbatar da wadatar kasar daga bukatun kayakin aikin likita da kuma magunguna.
Wannan zai hana fitar da kudade don sayarsu daga kasashen waje, sannan zai samarwa kasar kudaden shiga.
Mehdi Kadkhodazadeh, sakatren bangaren ilmin cututtukan hakora a ma’aikatar ilmi na kasar Iran ya ce ci gaban da aka samu a wannan ilmi ya rabu kasha uku, Akwai hanyar magance wani nau’in cutar hakori, da maganin kashe zafi a lokacin aikin kan hakora da kuma kayakin aikin haras da likitoci kan aikin hakora mai sauki sosai.