Sabuwar shugaban rikon kwarya na kasar Venezuela Delcy Rodriguez, ta bukaci tattaunawa da gwamnatin kasar Amurka a dai-dai lokacinda gwamnatin Trump take neman shuwagabannin kasar su mika kai ga bukatun Amurka ko kuma su kara fuskantar wasu sabbin hare-hare da kuma takurawa na tattalin arziki da siyasa.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa shugaba Delcy ta bayyana haka a yau Litinin a wani jawabin da ta gabatar wa mutanen kasar Venezuela da kuma gwamnatin kasar Amurka.
Wannan dais hi ne jawabin shugaban rikonkwarya na farko tun bayan da sojojin Amurka suka kama Madoro da matarsa a safiyar ranar Asabar da ta gabata.
Delcy ta ce caracas tana bukatar a muntunta ta kuma dauketa a matsayin kasa mai cikekken yenci a kuma bi hanyar diblomasiyya don magance matsalolin da suka taso tsakaninta da ta kasar Amurka.
Ta yi kira ga gwamnatin Amurka ta hada kai da gwamnatin Caracas don magance dukkan matsalolin da Amurka take ganin a kasar Venezuela. Ta ce kasar Venezuela da sauran kasashen yankin Latin Amurka basa bukatar yaki suna bukatar fahintar juna a cikin duk matsalolin da aka kasa warwaresu.
Tace kasar Venezuela tana bukatar zaman lafiya da kuma cikekken yenci a matsayin kasa ba kuma bayi ba.
Shugaban kasar Amurka ya bukaci gwamnatin kasar Venezuela ta bawa Amurka dukkanin abinda take bukata a kasar wadanda suka hada da dukkan filayen hakar man fetur na kasar da kuma wuraren hakar ma’adinai da sauransu. Kafin haka Marco Robio ya gargadi gwamnatin kasar Venezuela ta dauki matakan da suka dace na mikawa Amurka dukkan abubuwan da ta bukata a kasar Venezuela ko kuma ta fauskanci wasu karin aikin soje ko takurawa na tattalin arziki da siyasa.