Atriyanfar: Manufar Masu Adawa Da Juyin Musulunci Ba Za Ta Tabbbata Ba

Shugaban jam’iyyar ” Aiki Da Raya Kasa” Ta Iran  ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi manufofin ‘yan adawa ta tabbata a Iran. Muhammad

Shugaban jam’iyyar ” Aiki Da Raya Kasa” Ta Iran  ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi manufofin ‘yan adawa ta tabbata a Iran.

Muhammad Atriyanfar  wanda kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya yi hira da shi akan abinda yake faruwa a cikin kasar Venezuela, ya bayyana cewa; Ba abu ne mai yiyuwa ba a ce bayan gushewar shekaru fiye da 40 na juyin musulunci, wasu mutane masu adawa da juyi su tsallako iyaka su kafa wani sabon tsari.

Dan siyasar na kasar Iran ya kuma ce, babu yadda za a iya kwatanta tsakanin Venezuela da kuma Iran a cikin gida da kuma a fagen kasa da kasa.

Ya kuma kara da cewa; Venezuela kasa ce a yankin Latin kuma tana a karkashin yankunan da Amurka take da tasiri a cikinsu. Haka nan kuma  kasar tana da dimbin albarkatun man fetur wanda shi ne ya sa manyan kasashe su ka zama masu kwadayin shiga cikin kasar. A dalilin haka yanayin kasar Venezuela na musamman ne.

Dan siyasar na Iran ya kuma kara da cewa;  Ya zama wajibi mu dauki darussa daga abinda Amurkan take yin a cin zarafin kasashe masu ‘yanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted