A ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki, Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai wa kasar Lebanon hari a yankin ‘Mahafir’ dake tsakanin garuruwan Aytarun da Balida.
Sojojin Haramtacciyar kasar ta yahudawa sun yi amfani da makamin Phosphorus mai hayaki wanda aka haramta amfani da shi a duniya.
Haka nan kuma wani jirign sama maras matuki na sojojin mamayar ya kai hari a tsakanin garuruwan Tabnin da Jumaijumah da kuma Safad al-baddhikh da suke a kudancin Lebanon.
Tashar talabijin din ‘almanar’ ta bayar da labarin cewa; Sojojin sahayoniya sun Sanya wani shinge na wayoyin karfe a cikin kasar Lebanon da zurfin mita 150 a kusa da garin Yarun.
Sojojin kasar Lebanon da kuma rundunar MDD ta zaman lafiya “ Unifil” sun ga abinda “Isra’ilan’ ta yi, tare da shigar da shi cikin jerin laifukan da take yi na keta kudurin Majalisar Dinkin Duniya.